26 Disamba 2021 - 18:12
​Chadi: Sojojin Dake Mulki Sun Yi Wa ‘Yan Adawa Da Yan Tawaye Da Dama Afuwa

Majalisar sojoji dake mulki a kasar Chadi, ta amince da gagarimin rijaye da wasu daftarin dokoki guda biyu da suak tanayi yin afuwa gabadaya ga ‘yan tawaye da ‘yan adawa na kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannna na daya daga cikin bukatun da ‘yan adawa na kasar suka gindaya kafin zamnawa teburin tattaunawa ta kasa dake cikin shirin shugaban kasar Mahamat Idriss Deby.

Kudirin na farko ya shafi yafiya game da laifukan da suka shafi ta’addanci, makarkashiya, shigar da ‘yan samari a cikin gugun masu dauke da makamai.

Kudirin na biyu kuma ya shafi yi wa kasar zagon kasa, da kuma fadar albarkaci baki.

A cewar kakakin gwamnatin kasar Abderrahman Koulamallah, matakin ya shafi yin afuwa ga mutum 296.

Saidai a cewar ‘yan fafatukar kare hakkin dan adam a Chadin, matakin bai shafi kowa da kowa, illah kawai wasu zababu, saboda ‘yan tawayen kasar sun kai dubbai.

342/